Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kasuwar Galadima


Gabatarwa

Kasuwar Galadima guda ce daga cikin kasuwannin birnin Kano, wacce ta kafu sanadiyyar cikar ɗango da babbar Kasuwar Sabogari ta yi, kasuwar da titi ne kawai ya raba tsakaninsu.

Wannan kasuwa ta Galadima, kasuwa ce ta ƙasa-da-ƙasa duk da cewa mafiya yawan abokan hulɗarta daga ƙasashen Afirka suke musamman ma dai maƙwabtan Najeriya kamar irin su Chadi, Nijar da makamantansu.

Tsohon gwamnan Kano, marigayi Alhaji Abubukar Rimi shi ya gina wannan kasuwa a lokacin wa’adain mulkinsa da ya yi daga 1979 zuwa 1983 a matsayinsa na zaɓaɓɓen gwamnan Kano na farko sannan kuma a jamhuriyar siyasar Najeriya ta biyu. Wannan kasuwa a lokaci guda aka gina su tare da Kasuwar Dawanau. An tsungunnar da masu gudanar da sana’ar saye da kuma sayar da man girki da dukkan na’ukansa a wannan kasuwa.

Ana ganin wannan kasuwa ba za ta gaza shekaru talatin da bakwai da kafuwa ba. Kasantuwar shi marigayin ya yi mulkinsa ne daga shekarar 1979 zuwa 1983 a jamhuriyar siyasa ta biyu a tarayyar Najeriya. Kenan ko a shekararsa ta ƙarshen wa’adin mulkinsa ya ginata, to yau kasuwar tana da shekaru 37 (1982 – 2019) da kafuwa.

Hajoji

Ana sayar da nau’ukan kayayyakin da suka haɗa da manja, man gyaɗa, garin rogo, garin alabo, kifi - ɗanye da busasshe, naman dawa (Naman daji), iskar gas ta girki, sassan inji tahuna da kuma na babur da famfon ruwa da sauran kayayyaki masu tarin yawa.

Manazarta:


Tattaunawa da Alhaji Hassan Ƙoƙi, jami’in hulɗa da jama’a na 2 (PRO II) na ƙungiyar kasuwar a ranar 2 ga watan Janairun shekarar 2019.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub